Najeriya

Yan Najeriya sun fara tsokaci kan sabuwar tawagar ministoci

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Luc Gnago

Yan Najeriya sun fara mayar da martani kan jerin sunayen mutanen da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya gabatarwa majalisa, domin tantance su a matsayin ministocinsa.

Talla

Sunayen akasarin ministocin da suka yi aiki a wa’adi na farko sun bata, yayin da wasu sabbin mutane suka samu shiga.

Tsaffin ministoci 14 ne daga cikin 29 da shugaban ya gabatarwa majalisa suka samu dawowa.

Sai dai batun rashin baiwa matasa gurabe sosai da kuma mata ya dauki hankalin wasu daga cikin masu bibiyar lamurran kasar ta Najeriya.

Yayin nashi tsokacin kan sunayen ministocin a tattaunawarsa da sashin Hausa na RFI, Dr Aliyu Tilde yace babu laifi kan tawagar da shugaban Najeriyar ya mikawa majalisa, duk da cewa wasu an sa ran dawowar wasu tsaffin ministocin da sunayensu suka sake bayyana. Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren bayanin Dr Aliyu Tilde.

Dr Aliyu Tilde kan sabuwar tawagar ministocin Najeriya

Sai dai a nata bangaren babbar jam’iyyar adawa ta PDP, ta bayyana sabon jerin sunayen ministocin na shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, a matsayin tawagar da ke cike da mutanen da suka gaza sauke nauyin da aka taba dora musu a baya.

Jam’iyyar ta hannun sakataren yada labaranta, Kola Ologbondiyan ya ce babu kwarin gwiwa a tattare da sabuwar tawagar ministocin dangane da fatan magance kalubalen da Najeriya ke fuskanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.