Najeriya

Yan bindiga sun kaiwa kauyuka 70 farmaki a Sokoto

Yan bingida sun tashi kauyuka 70 a Sokoto.
Yan bingida sun tashi kauyuka 70 a Sokoto. Jakarta Globe

Yan bindiga dauke da makamai sun tashi garuruwa sama da 70 a jihar Sokoto da ke Najeriya, yayin da suka kashe mutane da dama tare da sace musu dukiya da suka hada da dabbobi.

Talla

Bayanai sun ce akasarin mazauna garuruwan da maharan suka afkawa sun samu mafaka a manyan garuruwa, domin tsira da rayuwarsu.

Yayin da yake yiwa sashin Hausa na RFI Karin bayani Sanata Ibrahim Gobir dake wakiltar yankin, ya ce tashin hankalin ya shafi Rabah, Goronyo sai kuma Isa da Sabon Birni.

Sanatan ya koka bisa yadda har yanzu al’ummar yankin ke ci gaba da fuskantar barzanar hare-haren ‘yan bindigar.

Kuna iya latsa lamar sautin da ke kasa domin sauraron Karin bayanin halin da ake ciki kan hare-haren na jihar Sokoto daga Sanata Ibrahim Gobir.

Sanata Ibrahim Gobir dake wakiltar yankunan da 'yan bindiga suka kaiwa farmaki a Sokoto

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya rawaito cewa a ranar 12 ga watan Yunin da ya gabata, rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar mutuwar mutane 8, sakamakon arrangamar da aka yi tsakanin wani gungun ‘yan bindiga da jami’an tsaron sa akai na Vigilante a karamar hukumar Isa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI