Najeriya

Ba zan sanar da wanda zai gaje ni ba- Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. PIUS UTOMI EKPEI / AFP

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, ba zai bayyana mutumin da zai gaje shi a karagar mulki ba bayan kammala wa’adinsa na biyu.

Talla

Buhari wanda aka rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun da ya gabata domin wa’adi na biyu, ya fadi haka ne a yayin karbar bakwancin mambobin Kungiyar Progressive in Academics a fadarsa da ke birnin Abuja.

Kungiyar ta bukaci shugaba Buhari da ya fara horar da matashin da zai gaje shi, amma shugaban ya ce, duk masu kaunar su gaje shi, to lallai su yi kokarin jajircewa kamar yadda shi ma ya yi.

A cewar Buhari, muddin ya ayyana mutumin da zai gaje shi, to zai haifar masa da tarin matsaloli, a don haka duk mai shaukin zama magajinsa, ya yi kokari ya zage dantse kamar yadda shi ma ya yi.

Shugaba Buhari ya tunatar da irin gwagwarmayar da ya sha ta tsayawa takarar shugaban kasa har sau uku ba tare da samun nasara ba, yayinda ya lashe kujerar shugaban kasar bayan ya tsaya takara karo na hudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI