Najeriya

Jam'iyyar AAC ta kori Omoyele Sowore

Omoleye Sowore
Omoleye Sowore Daily Post

Jam’iyyar African Action Alliance AAC ta kori shugabanta na kasa, Mr. Omoyele Sowore bayan kotun tarayya da ke birnin Abuja na Najeriya ta bayar da umarnin ci gaba da tsare shi har tsawon kwanaki 45 kafin kammala bincike game da zanga-zangar juyin juya halin da ya kira a wannan mako.

Talla

Kazalika Jam’iyyar wadda ke gudanar da taronta yanzu haka a Otel din Rockview da ke birnin Owerri, ta sallami wasu karin mambobinta 28, yayinda ta maye gurbin Sowore da Dr. Leonard Nzenwa.

Wannan na zuwa ne bayan mai shari’a Taiwo Taiwo na kotun tarayya ya bai wa Hukumar Tsaron Farin Kaya ,DSS umarnin ci gaba da tsare Sowore da ake zargi da aikata laifin ta'addanci.

Wasu hujjoji da Hukumar DSS ta gabatar wa kotun sun hada da hoton bidiyon da ke nuna Sowore na ganawa da Nnamdi Kanu, yayinda wani hoton bidiyon ya nuna wasu kalamansa da ke cewa, za su hada hannu da haramtacciyar Kungiyar ‘Yan Shi’a domin gurgunta gwamnatin kasar.

DSS ta ce, an kama Sowore ne saboda shirya zanga-zangar juyin juya halin da ya kira a duk fadin Najeriya da zummar nuna rashin amincewa da salon mulkin kasar.

Sowore shi ne mawallafin jaridar Sahara Reporters da ake wallafawa a yanar gizo,sannan ya tsaya takarar shugaban kasar karkashin jam’iyyar African Action Congress a zaben 2019 da shugaba Buhari ya lashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.