Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnan Zamfara ya tsige sarakunan gargajiya saboda barayi

Gwaman jihar Zamfara, Bello Matawalle
Gwaman jihar Zamfara, Bello Matawalle premiumtimesng
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 Minti

Gwamnan Jihar Zamfara da ke Najeriya, Bello Matawalle ya rattaba hannu kan tsige sarkin Maru, Abubakar Cika da kuma hakimin Kanoma, Lawal Ahmad bisa zargin su da taimaka wa ‘yan bindigan da suka kashe daruruwan jama’a.

Talla

A cikin watan Yunin da ya gabata ne, aka dakatar da sarakunan gargajiyar bayan zanga-zangar da jama’arsu suka gudanar don nuna bacin ransu kan yadda sarakunan ke hada kai da ‘yan bindigan masu kashe mutane.

Gwamnatin jihar Zamfara ta kafa wani kwamiti karkashin tsohon sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya, Mohammed Abubakar domin gudanar da bincike kan alakar sarakunan da barayin.

Tuni kwamitin ya samu sarakunan da gazawa, sannan kuma ya bayar da shawarar tsige su daga kujersru.

‘Yan bindiga dai sun kwashe wata da watanni suna kai hare-jare a jihar zamfara, abinda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.