Isa ga babban shafi
Najeriya

Sowore ya kalubalanci umarnin tsare shi na wa'adin kwanaki 45

Omoyele Sowore.
Omoyele Sowore. DR/saharareporters.com
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 Minti

Dan takarar shugabancin Najeriya a zaben da ya gabata, a karkashin jam’iyar AAC, Omoyele Sowore, ya shigar da kara gaban babbar kotun kasar dake Abuja, inda yake kalubalantar, hukuncin da ya baiwa jami’an tsaron DSS tsare shi tsawion kwanaki 45.

Talla

Sowore, wadda ya shirya zanga-zangar “RevolutionNow” ta neman juyin juya hali a Najeriya, ya ce tsare shin da aka yi ya sabawa kungin tsarin mulkin Najeriya da ya bashi ‘yanci.

A ranar 3 ga watan Agustan da muke ciki jami’an tsaron DSS suka kame Sowore, bayan kiran da yayi ga ‘yan Najeriya da su fita kwansu da kwarkwatarsu, don gudanar da zanga-zangar neman juyin juya hali, kiran da wasu suka amsa a sassan kasar, ko da yake zanga-zangar bata samu nasara ba.

Bayan kama shi ne kuma mai shari’a Taiwo Taiwo, a ranar Alhamis ya amsa bukatar hukumar tsaron DSS ta tsare Sowore har sai sun kamala bincike kan tuhumar cin amanar kasa da ake masa, sai dai mai shari’ar ya ce za a tsare shi ne tsawon kwanaki 45 a maimakon watanni 3 da hukumar tsaron ta DSS ta nema.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.