Najeriya

Zakzaky da mai dakinsa sun tafi India neman lafiya

Shugaban kungiyar ‘yan uwa Musulmi da aka fi sani da Shi’a, Shiekh Ibrahim El Zakzaky tare da mai dakinsa sun tashi daga filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja zuwa kasar India don neman maganin rashin lafiyar dake damun su.

Jagoran kungiyar ‘yan uwa Musulmi a Najeriya, da aka fi sani da Shi’a, Sheikh Ibrahim Zakzaky, tare da mai dakinsa Zeenat.
Jagoran kungiyar ‘yan uwa Musulmi a Najeriya, da aka fi sani da Shi’a, Sheikh Ibrahim Zakzaky, tare da mai dakinsa Zeenat. The Cable
Talla

Kakakin kungiyar ta mabiya Shi’a, Malam Musa Ibrahim ya tabbatar da hakan, yayin zantawa da sashin Hausa na RFI, inda ya kara da cewa El Zakzaky ya yi tafiyar ce tare da rakiyar wakilan gwamnati da kuma masu yi masa hidima.

Ranar 5 ga watan Agustan 2019, babbar kotun Najeriya da ke jihar Kaduna, ta baiwa shugaban kungiyar ‘yan uwa Musulmi da aka fi sani da Shi’a, Shiekh Ibrahim El Zakzaky da kuma matarsa Zeenat, damar fita zuwa birnin New Delhi na kasar Indiya don kula da lafiyarsa.

Kotun ta bada umarnin maido da Shiekh Zakzaky Najeriya domin ci gaba da fuskantar shari’a, da zarar asibitin da yaje sun sallame shi.

Yayin yanke hukuncin, mai Shari’a Darius Khobo, ya ce jagoran na mabiya Shi’a zai tafi neman lafiyar zuwa Indiya ne tare da rakiyar jami’an gwamnatin Najeriya.

Shiekh Ibrahim Zakzaky da matarsa Zeenat, na daga cikin daruruwan ‘yan kungiyar IMN ta ‘yan uwa Musulmi da jami’an tsaron Najeriya suka kema cikin shekarar 2015, bayan arrangamar da aka yi tsakaninsu da mabiya jagoran na Shi’a a garin Zaria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI