Ko an dinke baraka tsakanin Sarkin Kano da Ganduje?
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A karon farko cikin shekaru biyar an gudanar da hawan daba a masarautar jihar Kano kan idanun daya daga cikin shugabanin kasashen nahiyar Afrika wato shugaba Alpha Conde na kasar Guinea, wanda ya kasance babban bako. To sai dai kuma cikin wani yanayi na ba-zata, gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya halarci dukkanin haye-hayen da aka gudanar a masarautar, tun bayan da dangantaka ta yi tsami tsakaninsu. Ko hakan ya nuna cewa, babu sauran baraka tsakanin jagororin biyu? Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakken rahoton wakilinmu daga Kano, Abubakar Isa Dandago
Ko an dike baraka tsakanin Sarkin Kano da Ganduje?
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu