Shugaban kasar Guinea ya halarci hawan daushen sallah a Kano

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu kan rakumiyayin hawan daushe na babbar sallah,inda ya karbi bakwancin shugaban kasar Guenea Alpha Conde
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu kan rakumiyayin hawan daushe na babbar sallah,inda ya karbi bakwancin shugaban kasar Guenea Alpha Conde Aminiya|rfi

Masarautar Kano a Najeriya ta shirya kasaitaccen Hawan Daushe tare da halartar shugaban kasar Guinea Conakry Alpha Conde.

Talla

Conde wanda ya gudanar da sallar idi a garin Daura, a marecen jiya ya halarci bikin hawan sallar da aka yi a fadar mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi na biyu a Kofar Kudu.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya halarrci bikin karon farko tun bayan takaddama da suka samu da sarki Sunusi na biyu.

A bangare daya jami’an tsaro sun tarwatsa wasu gungun masu adawa da karin sabbin masarautu da gwamnatin jihar ta yi.

Kafin tarwatsa su, suna rera wakokin da ke cewa "sarki daya ne a Kano".

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI