Najeriya

Zakzaky da mai dakinsa sun koma Najeriya

Jagoran kungiyar ‘yan uwa Musulmi a Najeriya, da aka fi sani da Shi’a, Sheikh Ibrahim Zakzaky.
Jagoran kungiyar ‘yan uwa Musulmi a Najeriya, da aka fi sani da Shi’a, Sheikh Ibrahim Zakzaky. YouTube

Jagoran kungiyar ‘yan Shi’a ta Islamic Movement a Najeriya, Sheik Ibrahim El-Zakzaky da mai dakinsa Zeenat sun koma Najeriya daga Indiya, sakamakon rashin gamsuwa da matakan kula da lafiyarsu kamar yadda suka bukata.

Talla

A halin yanzu rahotanni sun tabbatar da cewa El-Zakzaky tare da mai dakin nasa na hannun jami’an hukumar tsaro ta DSS bayan isa Najeriya.

Wani hoton bidiyo da ofishinsa ya wallafa a shafin Twitter, ya nuna malamin na bayani kan musabbin komawarsa Najeriya, biyo bayan rashin jituwa tsakaninsa da likitocin da za su duba lafiyarsa da ta mai dakinsa a asibitin Medenta na Indiya.

Shugaban kwamitin fafutukar ganin gwamnatin Najeriya ta saki El-Zakzaky daga tsarewar da take masa, Abdullahi Musa, ya ce, an hana Sheik Zakzaky ganawa da likitocin da suka saba duba lafiyarsa a Najeriya, wadanda kuma ke da cikakkiyar masaniya kan lalurarsa.

Zalika kakakin kungiyar ta mabiya shi’a Ibrahim Musa ya zargi gwamnatin Najeriya da tin katsalandan kan shirin duba lafiyar jagoran nasu, abinda ya tilasta masa zabin komawa gida.

Sai dai tuni gwamnatin Najeriya ta musanta zargin, inda ta ce El-Zakzaky ne ya yi yunkurin karya sharuddan da aka gindaya masa, ta hanyar gabatar da wasu bukatu da suka hada, ajiye shi a babban Otal din da ke birnin New Delhi, zalika kada a yi masa shamakin ganawa da dukkanin bakin da suka nemi ziyartarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.