Najeriya

Rundunar 'yan sanda ta cafke jami'inta saboda caccakar gwamnati

Wasu jami'an 'yan sandan Najeriya.
Wasu jami'an 'yan sandan Najeriya. AFP/Luis TATO

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama wani jami’inta a jihar Yobe saboda yadda ya caccaki shugaban kasar Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo a shafinsa na Facebook, yana mai cewa, sun gaza.

Talla

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Yobe, AbdulMalik Sunmonu ya tabbatar da cafke Sunday U. Japheth, wanda ya soki hatta Sifeta Janar na ‘yan sandan kasar, sannan kuma ya yi barazanar kai harin ramuwar gayya kan sojoji biyo bayan kisan wasu jami’an ‘yan sanda da sojin suka yi a Taraba.

Jami’in dan sandan da aka cafke, ya kuma bukaci takwarorinsa da su gudanar da zanga-zanga a ranar 14 ga watan Agustan da ya gabata, a Adamawa, Yobe da kuma Maiduguri, don nuna bacin ransu, kan rashin biyansu albashi da wasu hakkokinsu.

A farkon watan Agusta, rundunar 'yan Sandan Najeriya ta bayyana cewa sojojin kasar sun kashe jami’anta 3 da kuma jikkata wasu da dama lokacin da suka kamo wani mai garkuwa da mutane akan hanyar Ibi zuwa Jalingo da ke Jihar Taraba.

Kakakin 'yan Sandan kasar Frank Mba ya ce, lamarin ya faru ne lokacin da sojojin suka bude musu wuta duk da gabatar da shaidar da ke nuna cewa, su jami’an 'yan sanda ne da ke gudanar da aikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI