Bakonmu a Yau

An samu raguwar hare- haren 'yan bindiga a jihar Zamfarar Najeriya

Sauti 03:36
Wadanda rikicin 'yan bindiga ya daidaita a Zamfarar Najeriya
Wadanda rikicin 'yan bindiga ya daidaita a Zamfarar Najeriya rfihausa

Rahotanni daga jihar Zamfara a Nigeria na nuna bisa dukkan alamu yanzu haka an sami shawo kan mummunar suna da jihar ta yi na kazaman hare-haren ‘yan bindiga da ake samu.Wannan na biyo bayan matakan da Gwamnan jihar Bello Matawalle ya dauka ne na janyo mutanen da ake zargi da kai hare-haren a jika don tattaunawa da su.Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Alhaji Ibrahim Isa Mayana tsohon Kwamishina kuma daya daga cikin dattawan jihar don jin yadda suka shawo kan lamarin.