Najeriya

Gwamnatin Najeriya tayi karin bayani kan dalilan maida Zakzaky gida

Jagoran mabiya Shi'a a Najeriya Shiekh Ibrahim El-Zakzaky.
Jagoran mabiya Shi'a a Najeriya Shiekh Ibrahim El-Zakzaky. PressTV

Gwamnatin Najeriya tayi karin bayani kan dalilin da ya sanya jagoran kungiyar ‘yan uwa Musulmi ta shi’a Shiekh Ibrahim Zakzaky da mai dakinsa komawa gida daga indiya, inda aka shirya duba lafiyarsu.

Talla

Gwamnatin Najeriya ta hannun ma’aikatar yada labaranta, ta ce matakin maido da El Zakzaky, ya biyo bayan kudurorin da ya yi nufin aiwatarwa, ciki har da tuntubar wasu kungiyoyin farar hula da wasu kungiyoyin mabiya akidar ta shi’a, domin neman mafaka da zummar gudun hijira zuwa wata kasa.

A gefe guda kuma gwamnatin Najeriyar ta ce mai dakin El Zakzaky wato Zeenat, tayi amfani da damar zuwa Indiyan wajen furta kalaman tunuzuri da suka kunshi, dora alhakin mutuwar ‘ya’yanta kan jami’an tsaron Najeriya domin muzanta kasar a idon duniya.

Sai dai kafin komawar Shiekh El-Zakzaky Najeriya, Shugaban kwamitin fafutukar ganin an sake shi daga tsarewar da ake masa, Abdullahi Musa, ya ce, an hana jagoran nasu ganawa da likitocin da suka saba duba lafiyarsa a Najeriya, wadanda kuma ke da cikakkiyar masaniya kan lalurarsa, abinda yasa suka zargi gwamnatin Najeriya da yin katsalandan kan shirin duba lafiyar jagoran nasu, abinda ya tilasta masa zabin komawa gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI