Najeriya

Lauyan Zakzaky ya maida martani kan komawar jagoran na Shi'a gida

Jagoran kungiyar ‘yan uwa Musulmi a Najeriya, da aka fi sani da Shi’a, Sheikh Ibrahim Zakzaky, tare da mai dakinsa Zeenat.
Jagoran kungiyar ‘yan uwa Musulmi a Najeriya, da aka fi sani da Shi’a, Sheikh Ibrahim Zakzaky, tare da mai dakinsa Zeenat. The Cable

Lauyan Shiekh El-Zakzaky, jagoran mabiya shi’a a Najeriya Femi Falana, ya ce tilas gwamnatin Najeriya ta gaggauta samar da mafita kan kula da lafiyar jagoran da mai dakinsa Zeenat.

Talla

Babban lauyan ya bayyana haka ne yayin shan alwashin garzayawa kotu don neman izinin sake fitar da jagoran na shi’a a Najeriya zuwa kasashen ketare don duba lafiyarsa.

A jiya Juma’a El Zakzaky ya koma Najeriya tare da mai dakinsa daga Indiya, bayan zargin sa da gwamnati tayi na, yunkurin kunyata ta a idon dunya, ta hanyar, tuntubar wasu kungiyoyin farar hula domin neman mafaka da gudun hijira zuwa wata kasa, zargin da malamin ya musanta.

Gabannin dawowarsa Shiekh El-Zakzaky, ya ce an hana shi ganawa da likitocin da suka saba duba lafiyarsa a Najeriya, abinda yasa shi zargin gwamnatin Najeriya da yin katsalandan kan shirin duba lafiyarsa, matakin da ya tilasta masa zabin komawa gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI