Isa ga babban shafi
Najeriya

Na fi samun 'yanci a Najeriya fiye da a kasar Indiya - El-Zakzaky

Jagoran mabiya Shi'a a Najeriya Shiekh Ibrahim El-Zakzaky.
Jagoran mabiya Shi'a a Najeriya Shiekh Ibrahim El-Zakzaky. AFP
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

Jagoran kungiyar ‘yan uwa Musulmi ta shi’a a Najeriya Shiekh Ibrahim El-Zakzaky ya ce yafi samun sakewa da ‘yanci a inda ake tsare da shi a Abuja, fiye da wanda ya samu a asibitin Medenta dake New Delhi babban birnin Indiya, inda shirin duba lafiyarsada ta mai dakinsa ya gagara.

Talla

A ranar Juma’a 16 ga watan Agusta, El-Zakzaky ya koma Najeriya, bayan zargin gwamnatin kasar da yin katsalandan kan shirin na duba lafiyarsa, inda ya ce an hana shi ganawa da likitocin da suke da cikakkiyar masaniya kan larurarsa.

Sai dai gwamnatin Najeriyar ta musanta zargin malamin, inda ta ce shi ne ya sana sharuddan daaka gindaya masa, ta hanyar tuntubar wasu kungiyoyin farar hula domin neman mafaka da gudun hijira zuwa wata kasa.

Tuni dai lauyan malamin  Femi Falana, ya ce tilas gwamnatin Najeriya ta gaggauta samar da mafita kan kula da lafiyar jagoran da mai dakinsa Zeenat.

Babban lauyan ya bayyana haka ne yayin shan alwashin garzayawa kotu don neman izinin sake fitar da jagoran na shi’a a Najeriya zuwa kasashen ketare don duba lafiyarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.