Najeriya

Boko Haram ta karbe garin Gubio na Borno

Wasu daga cikin mayakan Boko Haram
Wasu daga cikin mayakan Boko Haram News Ghana

Dubban mutane sun kaurace wa muhallansu, inda da dama daga cikinsu ke samun mafaka a dazuka sakamakon harin da Boko Haram ta kai tare da kwace iko da garin Gubio da ke Karamar Hukumar Gubio ta jihar Bornon Najeriya.

Talla

Wasu kwararan majiyoyi sun ce, maharan dauke da bindigogi da motocin yaki hudu sun dirar wa garin ne da yammacin ranar Laraba.

Rahotanni na cewa, mayakan sun gudanar da jam'in salloli a fadar hakimin garin Gubio, inda suka kirge motocin yakinsu a kusa da wurin da Gwamnan jihar, Farfesa Babangida Umara Zulum ya tsaya ya yi wa jama’a jawabi a ranar bikin Sallar layya da ta gabata.

A ziyarar da ya kai a wancan lokacin, Gwamnan ya lallashi mutanen da yawunsu ya zarce dubu 100 bayan sun yi haramar kaurace wa garin na Gubio sakamakon tashin hankalin Boko Haram.

Rahotannin sun ce, a halin yanzu mayakan na Boko Haram na rike da kananan hukumomi biyar a jihar ta Borno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI