Najeriya-Amurka

Najeriya ta bukaci 'yan damfara su mika kansu

Wani ma'aikaci yayin kidaya dalar Amurka a birnin Jakarta.
Wani ma'aikaci yayin kidaya dalar Amurka a birnin Jakarta. REUTERS/Beawiharta

Gwamnatin Najeriya ta hannun shugabar hukumar lura da ‘yan kasar mazauna kasashen ketare, Abike Dabiri-Erewa, ta bukaci, ‘yan Najeriya dake gida, wadanda Amurka ta samu da laifin damfarar Amurkawa miliyoyin daloli da su mika kansu.

Talla

Dabiri-Erewa ta yi gargadin cewa, muddin masu liafin suka noke, gwamnatin Najeriya zata tilasta mika su ga gwamnatin Amurka don fuskantar hukunci bisa laifukan da suka aikata.

A karshen makon nan hukumar binciken laifuka ta Amurka FBI, ta bayyana sunayen mutane 80, mafi akasarinsu yan Najeriya, da ta samu da laifukan damfarar yan kasar akalla dala miliyan 40, a tsakanin shekarar 2014 zuwa 2018.

Tuni dai jami’an hukumar ta FBI suka damke 17 daga cikin masu laifin dake zaune a birnin Los Angeles.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI