Najeriya-Amurka

Muna bibiyar karin 'yan damfara baya ga wadanda FBI ke nema - EFCC

Hukumomin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya sun bayyana cewa tuni suka kame mutane 28 kari kan wadanda hukumar FBI can a Amurka ta kame
Hukumomin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya sun bayyana cewa tuni suka kame mutane 28 kari kan wadanda hukumar FBI can a Amurka ta kame AFP Photo/MOHD RASFAN

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC, ta ce tana bibiyar wasu karin manyan ‘yan damfara, baya ga kusan guda 80 ‘yan Najeriya, da hukumar binciken laifuka ta Amurka FBI ta wallafa sunayensu.

Talla

Ofishin hukumar ta EFCC dake garin Ibadan ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai, inda tace yanzu haka jami’anta sun yi nasarar bankado wani asusu mai kunshe da akalla naira miliyan 223, da ‘yan damfarar suka samu ta hanyar kutsawa cikin bayanan sirrin da suka shafi asusun ajiya da kuma bayanan mutane daban daban a shafukansu na intanet.

Tuni dai hukumar ta EFCC ta bayyana kame mutane 28 daga cikin ‘yan damfarar da ake neman ruwa a jallo, bayan da suka yi awon gaba da miliyoyin dalolin Amurkawa.

A makon jiya hukumar binciken laifuka ta Amurka FBI ta wallafa sunayen ‘yan Najeriya kusan 80 da ta samu da laifin damfarar mutane dalar Amurka sama da miliyan 40, a tsakanin shekarun 2014 zuwa 2018, ta hanyar yanar gizo.

Yayin da ya ke karin bayani kan halin da ake ciki, shugaban hukumar na shiyyar Legas Muhammad Rabo, ya shaidawa manema labarai cewa, bayan hadin gwiwa da jami’an hukumar ta FBI, zuwa yanzu sun yi nasarar kame mutane 28 daga cikin ‘yan damfarar da Amurka ke farauta, yayinda suka kwato naira miliyan 486 daga hannunsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI