Zan kalubalanci gwamnan Rivers a kotu - Ganduje

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Kano State Government

Gwamnan Kano Abdull Umar Ganduje, ya sha alwashin kalubalantar takwaransa na jihar Rivers Nyesom Wike a kotu, biyo bayan rusa wani masallacin Juma’a da yayi a birnin Fatakwal.

Talla

Ganduje ya bayyana hakan ne cikin sanawar da sakataren yada labaransa Abba Anwar ya fitar.

Tuni dai gwamnan Rivers Nyesom Wike ya musanta zargin rusa Masallacin, da aka ce ya bada umarnin yi ranar 20 ga watan Agusta, inda ya ce wasu ne mutane ke yada jita-jitar don haddasa kiyayya tsakanin jama’a.

Sai dai har yanzu wannan batu na ci gaba da haifar da ce-ce-kuce, la’akari da cewa a gefe guda an rawaito gwamnan na furta kalaman bayyana jihar ta Rivers a matsayin mallakin wani addini guda, wanda kwanaki kalilan bayan hakan ne, labarin rusa masallaci a jihar ya bulla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.