Isa ga babban shafi
Najeriya

Karin 'yan bindiga sun mika makamansu a Zamfara

Karin 'yan bindiga sun ajiye makamansu a Zamfara.
Karin 'yan bindiga sun ajiye makamansu a Zamfara. REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 2

Karin ‘yan bindiga da suka tuba a jihar Zamfara dake tarayyar Najeriya, sun mika tarin makamai da suka hada da bindigogi da alburusai, da kuma kakin soja, ga jami’an tsaro.

Talla

Yayin tabbatar da tuban gungun ‘yan bindigar, Kakakin rundunar ‘yan sandan Zamfara Muhd Shehu, ya ce lamarin bangare ne na ci gaba da aiwatar da shirin kawo karshen tashin hankalin hare-haren ‘yan bindiga a jihar ta hanyar sulhu, a karkashin jagorancin gwamnati da Sarakunan gargajiya.

A watannin baya, Zamfara ke kan gaba tsakanin jihohin arewa maso yammacin kasar dake fama da hare-haren ‘yan bindiga da kuma satar mutane son karbar kudin fansa, sai dai a halin yanzu rahotanni sun nuna cewa an samu saukin matsalar tsaron a jihar ta Zamfara, biyo bayan yarjejeniyar sulhun da aka kulla da ‘yan bindigar.

A baya bayan nan gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa, mutane dubu 1 da dari 4 da 60 ne suka rasa rayukansu a hare-hare har guda 330 da ‘yan bindiga suka kaddamar a cikin watanni bakwai da suka gabata, musamman a yankunan Arewa maso yammacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.