Bakonmu a Yau

Tattaunawa da sarkin Kano Muhammadu Sunusi 2 kan rufe iyakokin Najeriya

Sauti 03:28
Sarkin Kano Sunusi Lamido Sunusi II
Sarkin Kano Sunusi Lamido Sunusi II

A Najeriya Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu, ya zargi kasashen da suka hada iyakoki da Najeriya da laifin rashin taimakawa Kasar a yakin da ta ke da masu fasa kwaurin haramtattun kayayyakin da ake shiga dasu Najeriya daga makwabtan kasashen.A cewar sa matakin rufe iyakokin yayi dai dai kuma zai taimaka wajen bunkasar tattalin Arziki, da kuma magance matsalar Tsaro.Yayin wata ganawa da yan jaridu a fadar sa ciki harda wakilin mu Abubakar Isah Dandago, sarkin na Kanon ya soma da yabawa shugaba Muhammadu Buhari game da kwamitin bada shawara kan tattalin Arzikin kasa daya nada.