Wasanni

Chukwueze ya zama dan wasa na 4 mafi tsada a La Liga

Samuel Chukwueze dan wasan Najeriya dake kungiyar Villarreal a Spain.
Samuel Chukwueze dan wasan Najeriya dake kungiyar Villarreal a Spain. Getty Images

Dan wasan gaba na Villarreal Samuel Chukwueze, ya zama dan wasa na 4 mafi tsada a ajin wadanda ke kasada shekaru 21, dake kungiyoyin gasar La Liga a Spain.

Talla

Rahotanni daga Spain sun ce a halin yanzu, darajar Chukwueze dan Najeriya ta kai fam miliyan 27, kwatankwacin naira biliyan 12, damiliyan 34 da kuma dubu 305.

A jiya laraba hukumar shirya gasar La Liga ta bayyana Samuel Chukwueze a matsayin dan wasa na 56 mafi tsada cikin 100 a Spain.

Matashin tauraron kungiyar Atletico Madrid Joao Felix da ya zo daga Benfica kan fam miliyan 113, shi ne dan wasa mafi tsada cikin ajin ‘yan kasa da shekaru 21 a La Liga, biye da shi kuma matasan ‘yan wasan Real Madrid ne Vinicius Junior a matsayi na biyu, da darajarsa take kan fam miliyan 63, sai kuma Rodrygo mai fam miliyan 36 a matsayi na uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.