Wasanni

Siasia na neman tallafin naira miliyan 36

Tsohon mai horas da 'yan wasan Najeriya, Samson Siasia.
Tsohon mai horas da 'yan wasan Najeriya, Samson Siasia. Reuters

Tsohon dan wasa zalika tsohon mai horar da tawagar kungiyar kwallon kafar Najeriya Super Eagles Samson Siasia, ya ce yana bukatar naira miliyan 36, domin daukaka kara kan hukuncin haramta mishi alaka da dukkanin al’amuran kwallon kafa har abada da FIFA ta yi.

Talla

Siasia yace yana bukatar makudan kudaden ne kafin cikar wa’adin ranar 10 ga watan Oktoba, wanda muddin lokacin ya wuce, to fa hukuncin da FIFA ta kakaba mishi zai tabbata, dan haka yake rokon gwamnatin Najeriya, da sauran masu hannu da shuni su kai masa dauki.

A ranar 25 ga watan Agusta, FIFA ta yanke hukuncin haramtawa Samson Siasia shiga al'amuran wasanni har abada, bayan samunsa da laifukan almundahana, ciki harda batun karbar na goro, domin shirya sakamakon wasanni, zargin da tsohon kocin na Super Eagles ya musanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.