Najeriya

'Gwamnonin Najeriya sun biya aikin hajji da kudaden talakawa'

Kimanin Musulmin Najeriya dubu 65 ne suka yi aikin hajji a bana a Saudiya
Kimanin Musulmin Najeriya dubu 65 ne suka yi aikin hajji a bana a Saudiya REUTERS/Zohra Bensemra

Wani binciken kwa-kwaf ya nuna cewa, gwamnatocin jihohin Najeriya sun kashe biliyoyn kudi daga asusun talakawa domin daukar nauyin mahajjata zuwa Saudiya da masu ziyarar ibada zuwa birnin Kudus a wannan shekarar duk da cewa har yanzu ba su biya albashin ma’aikata ba.

Talla

Daga cikin wadanda gwamnatocin suka dauki nauyinsu zuwa Makkah da birnin Kudus na Isra’ila sun hada da malamai da limaman coci da jami’an gwamnati da ’yan siyasa da jami’an kiwon lafiya da ‘yan uwa da abokan arziki kamar yadda jaridar Daily Trust ta bankado.

Bayanai na cewa, har yanzu gwamnatocin jihohin sun gaza biyan hakkokin ma’aikatansu na albashi duk da tallafin makuden kudaden da suka karba daga gwamnatin tarayya domin biyan albashin da sauran kudaden fansho.

Binciken ya kuma gano cewa, da dama daga cikin wadannan jijohin da suka dauki nauyin mahajjatan, sun yi watsi da manyan muhimman ayyukan ci gaban al’umma da ke bukatar kulawa ta musamman.

A bana dai, kudin aikin hajjin mutun guda daga Najeriya ya kai miliyan 1.5, yayin da na masu ziyarar ibada zuwa birnin Kudus ya kai kimanin Naira dubu 710.

Kodayake wasu gwamnonin sun sun ce, sun daina daukar nauyin mahajjatan, amma bincike ya nuna cewa, sun ci gaba da yin haka.

Sama da Musulman Najeriya dubu 65 ne suka gudanar da aikin hajjin bana a Saudiya, amma babu cikakkun alkalumman mabiya addinin Kirista da suka ziyarci birnin Kudus domin ibada daga Najeriya a bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.