Isa ga babban shafi
Najeriya - Birtaniya

Sa'insa ta barke tsakanin Jonathan da Cameron kan sace daliban Chibok

Tsohon Fira Ministan Birtaniya David Cameron, tare da tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, a Abuja cikin watan Yuli na shekarar 2011.
Tsohon Fira Ministan Birtaniya David Cameron, tare da tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, a Abuja cikin watan Yuli na shekarar 2011. Getty Images
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
2 min

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya karyata ikirarin tsohon Fira Ministan Birtaniya David Cameroon, wanda ya zarge shi da yin sakaci kan sace daliban makarantar Chibok, da kuma yin watsi da tayin gwamnatin Birtaniya na ceto daliban.

Talla

Sa’insa tsakanin shugabannin biyu ta soma ne bayan da David Cameron cikin wani sabon littafi da ya wallafa mai taken ‘For the Record’ ya zargi gwamnatin Jonathan da cin hanci da rashawa, da kuma kin amsa tayin rundunar sojin Birtaniya, na ceto daliban da mayakan Boko Haram suka sace ranar 14 ga watan Afrilu na 2014, a zamanin da yake Fira Minista.

Cikin littafin nasa, tsohon Fira Ministan na Birtaniya ya ce sojojin Birtaniya sun yi nasarar gano inda ake boye da da dama daga cikin daliban na Chibok da aka sace a waccan lokacin bayan amfani da na’urori zamani da jiragen yaki, amma Jonathan yayi kememe yaki amsa tayinsu na cika aikin kwato ‘yammatan, tare da bayyana lamarin a matsayin tuggun siyasa domin bata gwamnatinsa.

Sai dai yayinda yake karyata bayanan na Cameron, tsohon shugaban Najeriyar ya ce abin takaici ne irin wannan zargi ya fito daga bakinsa.

Goodluck Jonathan, ya ce a lokacin da lamarin ya auku, ya rubuta wasiku ga shugabannin manyan kasashe da suka hada da shi David Cameron din a lokacin da yake Fira Minista, shugaban Amurka a waccan lokacin Barrack Obama, shugaban Faransa Francois Hollande da kuma Fira Ministan Isra’ila Benyamin Netanyahu, inda ya nemi taimakonsu kan ceto daliban makarantar sakandaren ta Chibok.

Jonathan ya kuma kare kansa da cewar, a ranar 8 ga watan Maris na shekarar 2012, lokacin da mayakan Boko Haram suka sace wani dan kasar Birtaniya Chris McManus tare da abokin aikinsa Franco Lamolinara dan Italiya a jihar Sokoto, a matsayinsa na shugaban Najeriya, bai bata lokaci wajen baiwa dakarun Birtaniya damar ceto tuwaran ba, wadanda kuma suka yi nasara, da taimakon dakarun Najeriya. Saboda haka babu dalilin da zai sanya shi kin amsa tayin dakarun na Birtaniya wajen ceton Daliban Chibok.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.