Isa ga babban shafi
Najeriya

Yan bindiga sun sace daruruwan shanu da kayayyaki a Zamfara

'Yan bindiga sun sace daruruwan shanu a Zamfara.
'Yan bindiga sun sace daruruwan shanu a Zamfara. Information Nigeria
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 2

Rahotanni daga Zamfara a Najeriya sun ce ‘yan bindiga da adadinsu ya kai 300 haye kan babura, sun kutsa wasu yankunan kananan hukumomin jihar, inda suka sace kayayyakin abinci, kudade, man fetur da kuma shanu masu yawan gaske.

Talla

Wata majiya ta ce yan bindigar sun kai farmakin ne kan yankunan Mayanchi da Maru sai kuma Sunke dake karamar hukumar Anka.

A Mayanchi maharan, sun sace man fetur a babura gami da kudaden cinikin da gidan man yayi, inda daga nan suka fasa shaguna, tare da sace kayan abinci, kafin daga bisani su afkawa makiyaya tareda sace shanu da adadinsu ya kai 300.

Majiyar ta ci gaba da cewa a Sunke, ‘yan bindigar sun yiwa sojoji kwanton bauna, inda suka halaka wasu daga ciki, sai dai babu adadinsu a hukumance.

Jihar Zamfara ta shafe makwanni da dama ba tare da fuskantar hare-haren 'yan bindiga ba, sakamakon shirin yi musu afuwa da gwamnatin jihar ta kaddamar a karkashin jagorancinta, jami'an tsaro da kuma sarakunan gargajiya.

Daruruwan 'yan bindigar da suka addabi jihar ne dai suka mika makamansu ga gwamnati, tun bayan soma aiwatar da shirin sulhun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.