Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Barista Buhari Yusuf kan rikici tsakanin rundunar Yan Sanda da hukumar kula da ayyukan Yan Sandan

Sauti 03:32
Wasu jami'an 'yan sandan Najeriya.
Wasu jami'an 'yan sandan Najeriya. REUTERS/Austin Ekeinde
Da: Nura Ado Suleiman

Ganin yadda matsalar tsaro ta addabi Najeriya, shugaban kasar Muhammadu Buhari a shekarar da ta gabata, ya bada umurnin daukar Yan Sanda dubu 10, domin kara yawan jami'an tsaro da kuma maye gurbin wadanda suka yi ritaya da wadanda suka mutu.Sai dai ga alama shirin ya gamu da cikas, inda kusan shekara guda da bada umurnin, an kasa daukar Yan Sandan, saboda takun saka da kuma rikici tsakanin rundunar Yan Sandan kasar da kuma hukumar kula da ayyukan Yan Sandan.Rahotanni sun ce, kundin tsarin mulki ya baiwa hukumar Yan Sandan hurumin gudanar da aikin daukar sabbin Yan Sandan ne, amma kuma Hukumar Yan Sandan tace ita take da hurumin gudanar da aikin.Dangane da wannan rikici da ya hana gudanar da aikin, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Barr Buhari Yusuf, lauya mai zaman kansa, kan wannan dambarwa, kuma ga tsokacin da yayi akai.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.