Najeriya-Borno

Ambaliya ta mamaye gonakin shinkafa a Borno

Wani yanki na gonakin shinkafar da ambaliya ta mamaye a jihar Borno.
Wani yanki na gonakin shinkafar da ambaliya ta mamaye a jihar Borno. RFI/Hausa

Ambaliyar ruwa ta rutsa da daruruwan manoma a jihar Borno dake tarayyar Najeriya, inda ta lalata gonakin shinkafa masu yawan gaske.Kididdiga ta nuna cewar fadin kasar noman da ambaliyar ta mamaye ya zarta kadada dubu 2.Iftila’in ya zo ne a daidai lokacin da hare-haren mayakan Boko Haram suka hana mafi akasarin manoma a jihar ta Borno zuwa gonakinsu.Wasu dai na ganin cewa wannan ambaliya ba karamar barazana ba ce, la’akari da cewa za ta iya jefa jama’a cikin halin rashin abinci.Daga Maiduguri, Bilyamin Yusuf ya yi tattaki zuwa yankunan da lamarin ya shafa ya kuma aiko mana da rahoto akai.

Talla

Ambaliya ta mamaye gonakin shinkafa a Borno

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.