Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan sanda sun sake ceto mutane 108 daga gidan kangararru

Wasu da aka ceto daga gidan horas da kangararru a Najeriya.
Wasu da aka ceto daga gidan horas da kangararru a Najeriya. REUTERS/Stringer
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 2

‘Yan sandan Najeriya sun ceto wasu mutane 108 da ake tsare da su a wata cibiyar kula da kangararru a jihar Kwara.

Talla

Kakakin ‘yan sandan jihar Okansanmi Ajayi ya cesun kai samamen ne cikin garin Illorin, inda suka ceto maza 103 da kuma mata 5, wadanda shekarunsu ya kama daga 6 zuwa 45.

Samamen na wannan Juma’a shi ne na baya bayan nan da ‘yan sandan Najeriya suka kaddamar kan cibiyoyin gyaran halayyar kangararrun a sassan kasar, bayan umarnin hakan da gwamnati tayi.

A ranar laraba, jami’an tsaron a jihar Adamawa sun kwance wasu mutane 15 da aka daure su a daki guda.

A karshen watan Satumba, rundunar 'Yan sandan jihar Kaduna a tarayyar ta Najeriya ta ceto wasu mutane kimanin 300 da suka hada da manya da kananan yara, da ake tsare da su a wata makaranta dake unguwar Rigasa, da sunan koyar da tarbiya.

Kakakin ‘yan sandan Yakubu Sabo, ya ce daga cikin wadanda suka ceto akwai kananan yara guda 100 da shekarunsu basu fi tara ba, cikin mari, makare a wani karamin daki a ginin makarantar, da sunan basu tarbiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.