Najeriya

'Yan bindiga sama da 200 sun mika makamansu a Sokoto

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal tare da tawagar jami'an tsaro, yayin duba makaman da 'yan bindiga suka mika a jihar.
Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal tare da tawagar jami'an tsaro, yayin duba makaman da 'yan bindiga suka mika a jihar. TheCable

Gwamnatin jihar Sokoto ta ce akalla ‘yan bindiga 210 sun mika makamansu ga jami'an tsaro.

Talla

Yayin yiwa manema labarai karin bayani kan ci gaban Kwamishinan lura da sha’anin tsaro a jihar ta Sokoto, Garba Moyi ya ce ‘yan bindigar sun mikawa rundunar ‘yan sanda, makamai da dama da adadinsu ya kai 102.

Kwamishinan ya ce a karkashin shirin sulhun dake gudana, ‘yan bindigar sun kuma saki sama da mutane 30 dake hannunsu, da suka kunshi ‘yan Nijar, Zamfara da kuma Kebbi.

Wani karin bayani da gwamnatin ta Sokoto ta yi shi ne cewar cikin watanni uku da suka gabata, 'yan bindiga basu sake yin garkuwa da kowa a fadin jihar ba.

Sokoto na daga jihohin arewacin Najeriya da suka yi fama da matsalar yawaitar hare-haren 'yan bindiga dake satar dabbobi da kuma yin garkuwa da mutane.

Sai dai a baya bayan nan rahotanni sun ce an samu raguwar hare-haren 'yan bindigar sakamakon shirin sulhun da gwamnati ke jagoranta, a karkashin hukumomin tsaro da Sarakunan gargajiya a jihohin na Sokoto, Zamfara da kuma Katsina.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI