Najeriya-Adamawa

Ambaliya ta mamaye kauyuka a kananan hukumomin Adamawa 7

Wani sashi na daya daga cikin yankunan da ambaliyar ruwa ta mamaye a jihar Adamawa.
Wani sashi na daya daga cikin yankunan da ambaliyar ruwa ta mamaye a jihar Adamawa. News Agency of Nigeria (NAN)

Ambaliyar ruwa ta mamaye kauyuka masu yawan gaske a kananan hukumomi 7 daga cikin 21 na jahar Adamawa.Iftila’in ambaliyar ya biyo bayan saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka tafka a makon da ya gabata.Dubban mutane ne suka rasa muhallansu a sanadiyar ambaliyar, jami’an agaji sun bayyana ambaliyar ruwan a matsayin mafi muni da aka taba fuskanta a jihar Adamawa.Ahmad Alhassan ya yi tattaki zuwa wasu daga yankunan ambaliyar ta shafa, inda ya aiko mana da rahoto daga garin Yola.

Talla

Ambaliya ta mamaye kauyuka a kananan hukumomin Adamawa 7

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI