Najeriya

Shirin soji na tantance katunan shaidar jama'a ya haifar da korafi

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, yayin duba faretin sojojin kasar a garin Dansadau, 13/7/2016.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, yayin duba faretin sojojin kasar a garin Dansadau, 13/7/2016. STRINGER / AFP

Rundunar sojin Najeriya ta kaddamar da shirinta na tantance katunan shaidar jama’a a fadin kasar, wanda ta yiwa take da “Operation Positive Identification” a turance, matakin da ta ce, zai yi tasiri wajen zakulo mayakan Boko Haram da suka sauya matsugunansu zuwa wasu sassan kasar.

Talla

Mukaddashin daraktan yada labaran rundunar sojin Najeriyar, Kanal Onyema Nwachukwu, ya bukaci jama’a su kwantar da hankulansu, saboda shirin tantance katunan, ba zai yiwa na gari katsalandan a harkokinsu na yau da kullum ba.

Gabannin soma wannan shiri dai sai da Kwamitin Majalisar Wakilan Najeriya da ke kula da lamurran sojojin kasar, ya bukaci daukar lokaci domin wayar kan al’umma kafin fara aiwatar da shirin a dukkanin fadin Najeriya.

Baya ga korafin zauren majalisar wakilan Najeriya, kungiyoyin da suka hada da na hadin kan Yarbawa wato Afenifere da ta dattawan yankin Niger Delta sun caccaki shirin na soma tantance katunan shaidar jama’a da rundunar sojin Najeriyar ta kaddamar.

A ranar talata 5 ga watan Oktoba, babbar kotun Najeriya dake Legas za ta saurari karar da lauya mai rajin kare hakkin dan Adam Femi Falana ya shigar gabanta, inda yake neman ta soke shirin na “Operation Positive Identificaton”.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI