Injiniya Kailani Muhammad kan dokar sauya hulda tsakanin Najeriya da kamfanonin mai

Sauti 03:30
Hedikwatar kamfanin kula da albarkatun man Najeriya NNPC dake birnin Abuja.
Hedikwatar kamfanin kula da albarkatun man Najeriya NNPC dake birnin Abuja. REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya sanya hannu kudirin dokar aiwatar da sauye – sauye kan yarjeniyoyi da kasar ta kulla da manyan kamfanonin mai na kasashen waje da ke aiki a kasar, da zummar habaka kudin shiga da take samu daga danyen mai.Sai dai ba a bayyana lokacin da dokar za ta fara aiki ba, yayin da ake hasashen kamfanonin da abin ya shafa ba za su ji dadin wannan al’amarin ba.Kan haka ne Michael Kuduson ya tattauna da Injiya Kailani Mohammed, masani a harkokin da suka shafi man fetur.