Najeriya

'Yan kungiyar asiri sun halaka dalibai 13 a Kogi

Yan kungiyar asiri sun yi arrangama da juna a jihar Kogi.
Yan kungiyar asiri sun yi arrangama da juna a jihar Kogi. Jakarta Globe

Wasu ‘yan kungiyar asiri sun halaka akalla mutane 13 daga jihar Kogi da ke yankin tsakiyar Najeriya, yayin hare-haren da suka kaiwa junansu dasauran jama’a a tsakanin ranar Juma’a 1 ga watan Nuwamba zuwa ranar 4 ga watan.

Talla

Maharan sun kai farmaki ne a kan dalibai da ke Ayingba, inda suka rika saran daliban da ke karatu a jami’ar.

Da farko an bayyana cewa dalibai biyu ne suka rasa rayukansu, lamarin da ya harzuka sauran kungiyoyin asirin, wadanda suka shirya kai farmakin daukar fansa a kan bangaren da ake zargi da halaka mutanen 13.

Daga cikin wadanda aka halaka a fadan har da jagoran kungiyar asirin ta kwalejin kimiya da fasaha ta jihar Kogi da ke birnin Lokoja, kisan da aka alkanta da magoya bayan kungiyar asiri reshen jami’ar dake Ayingba.

Shaidu gani da ido sun ce daga jami’ar ne rikicin ya yadu zuwa titin da ake kira Stadium Road da kuma wata cibiya da ake kira “Our Lady Fatima Lodge” da ke birnin, inda aka kashe mutane da dama tare da cire gabobin jikinsu.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Kogi CP Hakeem Busari, ya tabbatar da faruwar rikicin, to sai dai ya ce dalibai uku ne suka rasa rayukansu a maimakon 13 da aka rawaito, yayin da ya ce suna farautar wadanda ke hannu a rikicin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI