Najeriya-Faransa

Karuwan Najeriya za su sha dauri a Faransa

Karuwan Najeriya sun mamaye kasar Faransa
Karuwan Najeriya sun mamaye kasar Faransa RFI

Wasu dillalan karuwai 24 ‘yan asalin Najeriya na fuskantar tuhuma a Faransa sakamakon zargin su da safarar mata domin tursasa musu shiga sana'ar karuwanci a kasashen Turai.

Talla

Binciken da aka gudanar a birnin Lyon na Faransa, ya nuna cewa, rabin karuwan birnin ‘yan asalin Najeriya ne, yayin da aka zargi wani fasto shi ma dan asalin Najeriya da bai wa karuwan goyon baya, inda har ma ya ba su wuraren zama.

Kazalika wasu alkaluma sun nuna cewa, ‘yan matan na Najeriya da ke karuwanci a Faransa, sun zarce takwarorinsu da suka zo daga China da kuma gabashin Turai

Sai dai bayanai na cewa, akasarin ‘yan matan na Najeriya sun shiga karuwancin ne bayan masu safarar su sun yaudare su cewar, za su  ba su ayyukan yi a Turai,  kamar gyaran gashi ko kitso da aikin tela da sauransu.

Amma daga bisani wadannan ‘yan mata na samun kansu dumu-dumu cikin aikin karuwanci domin samun kudaden da za su ci abinci da kuma biyan bashi.

A bara dai, an daure dillalan karuwai 15 har tsawon shekaru 11 a gidan yari saboda samun su da laifin tursasa wa matan Najeriya shiga karuwanci a Faransa.

Akasarin karuwan da ke balaguro zuwa Faransa sun fito ne daga yankin Benin na jihar Edo ta Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI