Najeriya

An sace man fetur na Dala biliyan 38 a Najeriya

Muhammadu Buhari, shugaban Najeriya.
Muhammadu Buhari, shugaban Najeriya. Twitter/Asorock

Hukumar Kula da Arzikin Karkashin Kasar da ake hakowa a Najeriya ta ce, kasar ta yi asarar man fetur da barayi suka sace da kudinsu ya zarce Dala biliyan 38 da rabi a cikin shekaru 10.

Talla

Alkaluman da hukumar ta bayar sun nuna cewar, daga cikin wannan adadi, an sace danyan man da ya kai na Dala biliyan 1 da rabi a cikin gida, da kuma tacaccen mai na kusan Dala biliyan 2 daga shekarar 2009 zuwa 2018.

Hukumar ta ce wadannan sace-sace na daga cikin matsalolin da suka shafi kudaden shigar da Najeriya ke samu, wanda ya nuna cewar a kowacce rana kawai ana sace man da ya kai na Dala miliyan 11, wato Dala miliyan 349 kenan a kowanne wata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI