Najeriya

Dakatar da kai mai iyakokin Najeriya zai gurgunta sadarwa - ALTON

Masu kula da layukan sadarwa a Najeriya sun yi gargadin fuskantar rashin kyawun layukan sadarwa a kan iyakokin kasar, saboda daina baiwa gidajan man dake yankunan man diesel.
Masu kula da layukan sadarwa a Najeriya sun yi gargadin fuskantar rashin kyawun layukan sadarwa a kan iyakokin kasar, saboda daina baiwa gidajan man dake yankunan man diesel. The Guardian Nigeria

Kungiyar ma’aikatan kamfanonin sadarwa a Najeriya ALTON, ta yi gargadin cewa, za a fuskanci rashin kyawun layukan sadarwa a sassan kasar dake kan iyaka, sakamakon dakatar da baiwa gidajan man dake yankunan man diesel.

Talla

Shugaban kungiyar ma’aikatan kamfanonin sadarwar Adebayo Gbanga yace tuni umarnin da dakatar da baiwa gidan mai a yankunan kan iyakar da hukumar Kwastam bada ya soma gurgunta ayyukan su.

Ranar laraba 6 ga Nuwamban da muke ciki, hukumar Kwastam din Najeriya ta baiwa jami’anta umarnin hana kai man fetur da kuma diesel ga ilahirin gidajen saida man da basu wuce nisan kilomita 20 daga kan iyakokin Najeriya da kasashe makwabta ba.

Ranar 20 ga watan Agustan da ya gabata, shugaban Najeriya Muhd Buhari, ya bada umarnin rufe iyakokin kasar na kan tudu, na wucin gadi, domin kawo karshen matsalar fasakaurin haramtattun kayayyaki zuwa ciki da wajen kasar, daga kasashe makwabta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI