Najeriya

Ciwon sanyi ya kashe yara dubu 162 a Najeriya

Za a iya magance cutar sanyin hakarkari ta hanyar allura riga-kafi
Za a iya magance cutar sanyin hakarkari ta hanyar allura riga-kafi REUTERS/Afolabi Sotunde

Cutar sanyin hakarkari da aka fi sani da Pneumonia a harshen Turanci, ta kashe kananan yara dubu 162 a Najeriya a bara kadai, yayin da a jumulce ta kashe yara dubu 802 a fadin duniya kamar yadda Kungiyar Agaji ta Save the Children ta sanar.

Talla

Rahotan da kungiyar ta fitar ya bayyana cewa, Najeriya ce kasa ta farko a duniya da ke da mafi yawan alkaluman yaran da suka rasa rayukansu saboda cutar.

Rahotan ya yi nazari ne kan yaran da ba su haura shekaru biyar ba da cutar ta lakume rayukansu a shekarar 2018.

Kasar Indiya ce ta biyu wajen samun asarar rayukan yaran sakamakon cutar, inda ta kashe dubu 127, sai Pakistan wadda ta rasa yara dubu 58, yayin da Jamhuriyar Demokradiyar Congo ta rasa dubu 40, sai Habasha da ta rasa dubu 32.

Babbar jami’ar Save the Children, Kevin Watkins ta bayyana Pneumonia a matsayin cutar da ta fi kashe kananan yara ‘yan kasa da shekaru 5, idan aka kwatanta da suaran cutuka a duniya.

Jami’ar ta ce, sai dai ba a mayar da hankali kan yaki da wannan cuta ba wadda za a iya magance ta ta hanyar allurar riga-kafi

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI