Nijar

An sauyawa daruruwan 'yan gudun hijira matsuguni a Nijar

Wasu yara a sansanin 'yan gudun hijira na Assaga dake kusa da Diffa a kudu maso gabashin Jamhuriyar Nijar.
Wasu yara a sansanin 'yan gudun hijira na Assaga dake kusa da Diffa a kudu maso gabashin Jamhuriyar Nijar. AFP

Sama da ‘yan gudun hijira 500 ne maza, mata da kuma yara kanana aka sauyawa sansani daga bakin iyaka zuwa garin Dan Daji Makau na gundumar gidan Runji.

Talla

Kimanin gidaje 86 ne aka kafa a wannan kauye don karbar ‘yan gudun hijirar da aka kafawa unguwa ta musaman.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira HCR reshen Maradi ce tare da taimakon kungiyar APBE ke aikin tsugunarda ‘yan gudun hijirar da suka bukaci a sauya musu wurin zama.

Garin Dan Daji Makau dai na da tazarar kilomita 7 daga Garin Gidan Runji.

Sansanin dake Dan Daji Makau shi ne na biyu bayan na garin Kaka mai mutane 700, kuma don cika ka’idoji ne hukumar ‘yan gudun hijirar ta HCR ta kafa su a tazarar nisan kilomita 50 daga iyakar Najeriya, inda ‘yan gudun hijirar suka fito.

Kan wannan katafaren aiki ne wakilinmu Salisu Isa ya aiko mana da cikakken rahoto, bayan halartar garin na Dan Daji Makau.

An sauyawa daruruwan 'yan gudun hijira matsuguni a Nijar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI