APC zata shiga zaben Bayelsa-INEC

Shugaban hukumar shirya zaben Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu
Shugaban hukumar shirya zaben Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu RFI hausa

Hukumar Zabe a Najeriya tayi karin haske dangane da hukuncin wata kotu na cewa Jam’iyyar APC bata da dan takara a zaben Gwamnan Jihar Bayelsa da zai gudana gobe asabar.

Talla

Wata kotu a ranar Alhamis ta yanke hukunci kan karar da Sanata Heineken Lokpobiri ya shigar inda yake kalubalantar yadda Jam’iyyar su ta APC ta gudanar da zaben fidda gwani da ya baiwa David Lyon nasara, inda tace an saba ka’ida wajen gudanar da zaben.

Mai shari’a Jane Inyang tace rashin bin ka’idar gudanar da zaben fidda gwani ya nuna cewar Jam’iyyar APC bata da dan takara a zaben na ranar Asabar.

Kakakin hukumar zabe Aliyu Bello yace wancan hukunci ya shafi rikici ne na cikin gida, amma Jam’iyyar APC na cikin jam’iyyun da zasu fafata a zaben na gobe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.