Najeriya

Zaben Kogi: Yahya Bello ya yi tazarce

Gwamnan jihar Kogi Yahya Bello tare da shugaban jam'iyyar APC na kasa Adams Oshoimhole da mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo.
Gwamnan jihar Kogi Yahya Bello tare da shugaban jam'iyyar APC na kasa Adams Oshoimhole da mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo. Premium Times Nigeria

Hukumar zabe a Najeriya ta bayyana Yahaya Bello a matsayin zababben Gwamnan Jihar Kogi, sakamakon zaben da aka gudanar a karshen mako.

Talla

Baturen zaben da ya tattara sakamako, Farfesa Ibrahim Garba, shugaban Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, yace Bello na Jam’iyyar APC ya samu kuri’u 406,222, yayin da Engr Musa Wada na Jam’iyyar PDP ya zo na biyu da kuri’u 189,704.

Farfesa Bello yace ganin Yahaya Bello ya cika dukkan sharuddan da dokokin zabe suka tanada, ya zama zababben gwamnan Jihar Kogi.

Sai dai kungiyoyin sa ido sun koka kan yadda zaben na Kogi ya gudana, saboda amfani da Yan bangar siyasa da kuma razana masu kada kuri’u.

A sanarwar da masu sa ido daga kasashen Amurka da Birtaniya da Jamus da Ireland da Nertherlands da kuma kungiyar kasashen Turai suka sanya hannu, sun bayyana damuwa kan yadda aka gudanar da zaben da kuma irin tashin hankalin da aka gani.

Sanarwar ta bayyana matukar damuwa irin tashin hankalin da aka gani a zabukan guda biyu da akayi a Najeriya, wato a Jihohin Bayelsa da Kogi da kuma yadda aka dinga cinikin kuri’u a bainar jama’a da kwace akwatunan kada kuri’u.

Kasashen sun bukaci Najeriya ta inganta harkokin tsaron ta wajen samarwa Yan kasar yanayi mai kyau da zasu kada kuri’un su ba tare da samun tashin hankali ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI