Al'adun Gargajiya

Makomar sana'ar magungunan gargajiya: Gado Ko Haye?

Wallafawa ranar:

Shirin Al’adun Mu Na Gado a wannan makon, ya waiwayi bangaren magungunan gargajiya ne, musamman kan wani babban taro na kasa da masu wannan sana’ar suka gudanar a garin Bauchin Nigeria, domin duba makomar wannan sana’ar da a baya ake dangantawa da gadon iyaye da kakanni, amma kuma yanzu yawanci ake yiwa shigar burtu. A da dai magungunan gargajiya sai gidan wane da wane watau ko dai Wanzamai, Masunta, Mafarauta, ko kuma Unguwar-zoma.

Agbetuya Samuel, wata mai maganin gargajiya yayin ciniki da masu saye a shagonta dake kasuwar garin Akure a jihar Ondo dake Najeriya. 28/8/2019.
Agbetuya Samuel, wata mai maganin gargajiya yayin ciniki da masu saye a shagonta dake kasuwar garin Akure a jihar Ondo dake Najeriya. 28/8/2019. REUTERS/Afolabi Sotunde
Sauran kashi-kashi