Ahmed Musa ya dauki nauyin karatun 'yan Najeriya 100 a Jami'a

Dan wasan tawagar Super Eagle ta Najeriya Ahmed Musa yayin wasa a Klob din sa dake Saudi Arabiya
Dan wasan tawagar Super Eagle ta Najeriya Ahmed Musa yayin wasa a Klob din sa dake Saudi Arabiya rfi

Kaftin din Super Eagles Ahmed Musa ya sanar da cewa zai dauki nauyin dalibai har 100 a wata jami'a mai zaman kanta da ke birnin Kano a Najeriya.

Talla

Ahmed Musa ya bayyana haka ne a yayin wata ganawa da ya yi da wakilan jami'ar Skyline University Nigeria dake birnin Kano, inda ya sanya hannu kan wata yarjejeniyar zama Jakadar jami'ar na musamman.

Ahmed Musa ya ce yana matukar kaunar harkokin ilimi kuma dalilin da ya sa ya shiga yarjejeniyar kenan.

"Wannan ne yasa na dauki nauyin dalibai 100 a wannan jami'ar," kamar yadda ya bayyana a shafin sa na Instagram.

Tuni al'ummar Najeriya suka fara yaba matakin fitattun kasar wajen maida hankali kan ci gaban ilimi.

A baya-bayan nan shima tauraron shirya fina-finan Hausa, kuma mawaki Adam A Zango ya biyan kudin karatun wasu dalibai 101 na shekara uku, a makarantar Farfesa Ango Abdullahi dake Zaria, inda ya kashe fiye da naira miliyan 46.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.