Alhaji Abubakar Mairamri tsohon Kwamishinan 'yan sanda kan umurnin Muhammadu Buhari na kawo karshen matsalolin tsaro a Najeriya

Sauti 03:08
Shugaba Muhammadu Buhari sanye da kakin soji tare da rakiyar mukarrabansa,yayin wata ziyara a jahar Borno
Shugaba Muhammadu Buhari sanye da kakin soji tare da rakiyar mukarrabansa,yayin wata ziyara a jahar Borno saharareporters

A karon farko Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a fusace ya bukaci jami'an tsaron kasar da kada su kuskura su sassautawa masu garkuwa da mutane da ‘yan ta'adda da suka buwayi sassan kasar yanzu haka. Buhari ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mataimakinsa na musamman kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar,yana mai cewa babu yadda zai bar ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane na yadda suka ga dama a kasar.Dangane da wannan batu, Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Alhaji Abubakar Mairamri tsohon Kwamishinan ‘yan Sanda a Najeriya.