Kotunan Najeriya sun tabbatar da zaben gwamnonin Kano da Sokoto

Kotunan daukaka kara sun tabbatar da gwamnonin Kano da Sokoto a kujerun su
Kotunan daukaka kara sun tabbatar da gwamnonin Kano da Sokoto a kujerun su RFI/Hausa

Kotun daukaka kara da ke zama a Kaduna ta tabbatar da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a matsayin sahihin wanda ya rashe zaben da aka gudanar, inda ta yi watsi da karar da Abba Kabir da kuma PDP suka gabatar mata.

Talla

Tun a ranar 8 ga watan Nuwamba ne kotun ta fara sauraron karar, wadda PDP ta daukaka bayan kotun sauraron kararrakin zabe ta yi watsi da ita a shari'ar da mai Shari'a Halima Shamaki ta jagoranta.

Alkalin kotun Mai Shari'a Tijjani Abubakar ya ce hukuncin da kotun baya ta yanke ya inganta kuma Abdullahi Umar Ganduje ne ya ci zaben.

Yanzu haka dai jami'iyyar Adawar kasar PDP da dan takarar ta na da damar rugawa zuwa kotun kolin kasar, amatsayin damar karshe.

A bangare daya kuma wata kotun daukaka karar ta tabbatar da Aminu Waziri Tambuwal na PDP din a matsayin gwamnan jihar Sokoto, bayan watsi da karar da APC ta shigar gabanta.

Kotun ta yi watsi ne da karar da jam'iyyar APC da dan takararta Ahmad Aliyu suka shigar suna kalubalantar nasarar da Gwamna Aminu Tambuwal na PDP ya samu a zaben gwamna na 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.