Najeriya-Buhari

Ba ni da shirin neman wa'adi na 3 a mulkin Najeriya- Buhari

Nigerian President Muhammadu Buhari and Vice President Yemi Osinbajo
Nigerian President Muhammadu Buhari and Vice President Yemi Osinbajo dailypost.ng

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ba shi da nufin ci gaba da mulkin kasar bayan karewar wa’adinsa a shekarar 2023 duk da jita-jitar da ke bayyana cewa shugaban na kokarin samar da gyara a kundin tsarin mulki da zai sahale masa ci gaba da mulki.

Talla

Cikin jawabansa yayin taron Majalisar Jam’iyyar APC a Abuja da ya gadana ranar Juma’ar da ta, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba shi da sha’awar aiwatar da wani gyara da zai sahale masa karin wa’adi akan karagar mulki.

Kundin tsarin mulkin Najeriya dai wa’adi 2 na shekaru hurhudu ya tanadarwa mukamin gwamna da shugaban kasa karkashin tsarin dimukradiyya.

Cikin jawabin nasa Muhammadu Buhari ya bukaci mambobin Jam’iyyarsa ta APC su yiwa kundin tsarin mulkin kasar karatun ta-nutsu tare da gano ka’idojin da aka gindayawa shugaban kasa da kuma gwamnoni gabanin fara nuna bukatar sake tsayawarsa shugabanci a wa’adi na 3.

Kalaman na Muhammadu Buhari na neman tabbatar da jita-jitar da ke nuna yadda wasu mambobin jam’iyyar ta APC ke neman shugaban ya amince da gyara a kundin tsarin mulki da zai bashi damar dorawa a wa’adi na 3 na mulkin kasar.

Ko a shekarar 2006 gab da karkarewar wa’adin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo sai da ya bukaci gyaran kundin tsarin mulki don bashi cikakkiyar damar kai wa ga wa’adi na 3 a mulkin Najeriyar amma Majalisar kasar ta yi fatali da bukatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI