Kano

Ganduje ya rattaba hannu kan dokar sabbin masarautun Kano

Gwamnan Jihar Kano da ke Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya rattaba hannu kan dokar kirkirar sabbin masarautu hudu bayan Majalisar Dokokin Jihar ta amince da dokar a ranar Alhamis.

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Kano State Government
Talla

Cikin gaggawa ‘yan Majalisar suka amince da wannan doka a ranar Alhamis duk da cewa babbar kotun jihar ta soke sabbin masarautun tare da dakatar da sarakunan da gwamnan ya nada.

Shugaban masu rinjaye a Majalisar dokokin, Labaran Abdul-Madari ya ce, manufar kirkirar sabbin masarautun, ita ce bunkasa ci gaba a fadin jihar, kuma a cewarsa, sun dauki matakin ne domin talakawa.

A shekarar da ta gabata ne, gwamna Ganduje ya kirkiro masarautun, matakin da ake kallo a matsayin yunkurin rage karsashin Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi wanda ake ganin ba sa jituwa saboda wasu dalilai na siyasa.

Sabbin masarautun sun hada na Bichi, karkashin Aminu Bayero. sai ta Rano, karkashin Tafida Abubakar-Ila da ta Karaye wadda aka bai wa Ibrahim Abubakar, sai kuma ta Gaya, karkashin Ibrahim Abdulkadir.

Da dama daga cikin al’ummar Kano har ma da wasu ‘yan Najeriya sun caccaki wannan mataki na samar da sabbin masarautun, inda suke ganin, hakan zai haddasa rarrabuwar kawuna tsakanin al’umma.

ABUBUWAN DA SABUWAR DOKAR TA KUNSA

Kadan daga cikin abubuwan da sabuwar dokar masarautun jihar Kano ta kunsa:

1- Bai wa gwamna cikakkiyar damar nada sarakuna da kuma masu nada sarki wato Kingmakers.

2- Dole ne kowacce masarauta ta mika wa gwamnatin jihar kasafin kudinta domin anincewa akan yadda za ta kashe kudinta.

3- Gwamna na da ikon rage darajar kowanne sarki a Kano daga sarki mai Daraja ta daya zuwa mai Daraja ta biyu ko ta uku idan bukatar hakan ta kama. 

4- Gwamna zai iya tsige sarki idan har sarkin ya kaurace wa zaman Majalisar Sarakunan Jihar Kano wadda za a kafa nan gaba, idan har yai hakan ba tare da wani dalili kwakwara ba.

5- Sarakunan za su iya bai wa gwamnatin jihar shawara amma sai sun nemi izinin gwamna.

6- Kowanne Sarki dole ne ya kiyaye yin abin da zai zubar da mutunci da martabar al'ummarsa a idon duniya.

A yayin rattaba hannu kan dokar, Ganduje ya gargadi sarakunan da su kiyaye ka'idojin da aka gindaya domin duk wanda ya keta su, gwamnati za hukunta shi. Gwamnan ya kuma  ja kunnen hakimai na sababbin masarautun, inda ya ce, kowannensu ya yi wa sarkinsa mubaya'a ko kuma ya rasa rawaninsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI