Rashin kirkirar masarautu shi ya fi alheri a Kano- Daurawa
Wallafawa ranar:
Fitaccen malamin addinin Islama a Najeriya, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bukaci gwamnatin jihar Kano ta gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’a kafin yin gaban kanta wajen kirkirar sabbin masarautu a jihar.
A yayin zanta wa da sashen Hausa na RFI, Sheikh Daurawa ya ce, suna ganin rashin kirkirar sabbin masarautun shi ya fi alheri domin kauce wa wargaza kawunan al’umma.
Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar da muka yi da Sheikh Daurawa.
SHEIK DAURAWA KAN MASARAUTU A KANO
Tuni Majalisar Dokokin Jihar ta amince da dokar kirkirar sabbin masarautunu bayan gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar da kudirin dokar ga Majalisar.
Cikin gaggawa ‘yan Majalisar suka amince da wannan doka a ranar Alhamis duk da cewa babbar kotun jihar ta soke sabbin masarautun tare da dakatar da sarakunan da gwamnan ya nada.
Shugaban masu rinjaye a Majalisar dokokin, Labaran Abdul-Madari ya ce, manufar kirkirar sabbin masarautun, ita ce bunkasa ci gaba a fadin jihar, kuma a cewarsa, sun dauki matakin ne domin talakawa.
A shekarar da ta gabata ne, gwamna Ganduje ya kirkiro masarautun, matakin da ake kallo a matsayin yunkurin rage karsashin Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi wanda ake ganin ba sa jituwa saboda wasu dalilai na siyasa.
Sabbin masarautun sun hada na Bichi, karkashin Aminu Bayero. sai ta Rano, karkashin Tafida Abubakar-Ila da ta Karaye wadda aka bai wa Ibrahim Abubakar, sai kuma ta Gaya, karkashin Ibrahim Abdulkadir.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu