An kai wa Ministan Najeriya hari a Spain
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Wasu ‘yan Najeriya mazauna kasar Spain sun kaddamar da hari kan Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi a daidai lokacin da yake halartar taron sauyin yanayi a birnin Madrid a wannan Juma’a.
Mista Amaechi wanda ya sanar da aukuwar lamarin a shafinsa na Twitter ya ce, jami’an ‘yan sandan Spain sun fatattaki maharan kafin yi masa lahani.
Ministan ya bayyaan cewa, yana cikin koshin lafiya, yayin da ya mika godiya ga masu yi masa addu’a da kuma nuna masa goyon baya.
Kawo yanzu ba a tabbatar ko maharan mambobin kungiyar IPOB ne wadda ke fafutukuar kafa kasar Biafra a Najeriya ba.
Ko a 'yan kwanakin baya, sai dai aka kai makamancin wannan harin kan Sanata Ike Ekweremadu a daidai lokacin da yake halartar taro a kasar Jamus, yayin dakungiyar IPOB ta dauki alhakin harin a wancan lokaci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu