Najeriya

Sanata Kalu zai ci gaba da karbar albashi daga gidan Yari

Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu.
Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu. Sahara Reporters

Majalisar Dattawan Najeriya ta ce, mai tsawatarwar zaurenta, Sanata Orji Kalu, zai ci gaba da karbar albashinsa da sauran kudadensa na alawus-alawus duk da cewa yana tsare a gidan yari.

Talla

A makon jiya ne babbar kotun tarayya da ke birnin Lagos ta yi wa Sanata Kalu daurin shekaru 12 a gidan kaso bayan ta same shi da laifin handame Naira biliyan 7.65.

Hukuncin daurin da aka zartas kan tsohon gwamnan na Abia ya zo ne shekaru 12 bayan kamun farko da jami’an hukumar EFCC suka yi masa a shekarar 2007, aka kuma gurfanar da shi gaban kotu, tare da Daraktan tafiyarda harkokin kudin gwamnatin jihar Abia Udeh Udeogu, a zamanin jagorancin Kalu.

Majalisar ta ce, har yanzu Kalu na kan kujerarsa ta Sanata har sai an mika batunsa ga kotun koli, wadda za ta bada hukuncin karshe kan laifun da babbar kotun ta ce, ya aikata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI